GASA, GASA, GASA!-Akwai kyautar Katin Waya

GASA, GASA, GASA!
Ga wata gasa na zo mana da shi, mai saukin gaske, kuma ga duk wanda ya ci gasar yana da kyautar katin N500 na network din da kake so (kana iya fin karfin katin saboda 'karancinsa) amma na saka ne saboda karfafa abin da zan yi gasar a kai.
Wasu Jawaban Shaikh Zakzaky na yanko guda biyu wanda ya gudanar da su a wurare mabambanta. Zan saka Jawabin a kasa domin a fada min a ina aka yi Jawabin?Wacce rana? Sannan a wani gari? A wani taro?

SHARADIN SHIGA GASAR
1. Za a yi la'akari ga wanda ya fara amsa tambayoyin gasar a cikin 'comments'
2. Ka natsu kafin ka amsa, duk wanda ya yi 'Editing' amsarsa ya fadi.
3. Ka'idar gasar shi ne daga yanzun karfe 11:45am zuwa karfe 9:00pm (na daren yau 3/2/2018).
4. Idan aka yi la'akari ba wanda ya amsa tambayoyin guda biyu. Za a yi la'akari da wanda suka amsa tambaya daya suka fadi daya shima duba da wanda ya fara ba da amsa sai a raba katin gida biyu.
Ga Jawaban nan guda biyu a kasa.
TSAKANIN SHUWAGABANNI, TALAKAWA DA MALAMAI
“Al’umma tana da matsala, wannan sananne ne. Kuma idan akwai matsala ya kan dau kowane janibi, kowanne bangare. Da Shuwagabanni da talakawa duk suna da laifi. Amma kasan su Shuwagabanni su aka ba alhakin abubuwa da dama, idan basu tsaya da na su ba, Talakawa ba yadda suka iya. Saboda haka akwai laifi na wadanda amanar al’umma din ke hannunsu. Wannan dukiya da jinainai na mutane, wadanda yake su, ga dukkan alamu ba sun dauka amana ba ne. Su sun dauka kamar kayan su ne (na kashin kansu). Basu dauka kuma za a tambayesu dangane da shi ba. Shiyasa ake samun matsala dangane da wannan. Saboda hatta su Shuwagabannin ba su dauka amanar mutane ne da dukiyarsu aka basu ba. Saboda haka sun dauka kayan su ne. Sai yadda suka yi. Ka ga nan ne aka samu matsalar Shugabanci kenan. To kuma ka yi magana dangane da sha’anin Malamai, sai kuma ya zama har wala yau, suma Malamai suna da na su abin da ya kamata a ce ya zama sun yi idan suka ga Shuwagabanni sun kauce. To, ba kamata ya yi su bisu a kauce din ba. Ya zama lazim su gaya musu gaskiya. Kuma ma har in zai yiwu a yi baram-baram ne, sai dai a yi. Amma kuma sai ka ga da yawa suna biye da su. Harma su Shuwagabannin suna ganin suke da shugabanci akan Malamai din.”
A SIFFANTU DA KOYARWAR ALKUR’ANI
“madaukin Alkur’ani ba kawai wanda ya dauke shi a kwakwalwa ne ba, wanda ya dauke shi a zuciya da jiki, wanda yake maganarsa Alkur’ani, dabi’o’insa Alkur’ani. Shi ne wanda yana siffatantuwa siffan Alkur’ani. Wannan shi ne ‘Hamilul Kur’an.’ Na’am ba za ka zama ‘Hamilul Kur’an’ ba, sai idan ka dauki haruffansa (awwalan). Haruffansa zaka iya karantawa daga farko zuwa karshe da ka. Matakin farko ne wannan. Sannan kuma mataki na biyu, a ganka a ga dabi’ar Alkur’ani. Wannan shi ne Babban kule (kalubale), bayan kiyaye haruffan Alkur’ani, to, kiyaye shi har ya zama dabi’arka Alkur’ani. Ka yi ‘unsi’ da Manzon Rahma (saww). Wanda aka ruwaito an ce; “dabi’arsa Kur’ani ne!”
Tambayoyin sune:
A ina aka yi Jawabin? Wacce rana? Sannan a wani gari? A wani taro?
Sai na ji daga gare ku. Gasar bude yake ga kowa da kowa.
Na ku a koyaushe Ammar Muhammad Rajab
3/2/18

Comments