Fitaccen Masanin Harshen Hausa Daga Jami'ar Bayero, Kano Ya Rasu

Fitaccen masanin harshen Hausa Mu'azu Sani Zaria ya rasu

 

Allah ya yi wa fitaccen masanin harshen Hausan nan na Jami'ar Bayero ta Kano da ke Najeriya, Farfesa Mu'azu Alhaji Zaria Sani rasuwa ranar Juma'a.
Farfesa M.AZ., kamar yadda aka fi saninsa, ya rasu ne a birnin na Kano bayan ya yi fama da rashin lafiya.
 
Masanin ya yi fice wajen ilimin sarrafa harshe da nahawun Hausa. Ya yi karatunsa a Najeriya da Ingila. Farfesa Mu'azu Sani Zaria ya yaye dubban dalibai da suka yi nazari kan ilimin tsarin sauti da harshen Hausa da ma Turancin Ingilishi. Kazalika ya rubuta littattafai da dama.


Farfesan ya rasu ya bar mata biyu da 'ya'ya 11 -- mata hudu, maza bakwai da jikoki biyar.

Comments