HALIN DA MUSULMAN BAMA KE CIKI
Daya daga cikin abokan sada zumunta na 'Facebook' Zeynab Muzzafar ta kawo rahoto mai ban tausayi a yau dangane da halin da Musulman kasar Bama ke ciki.
A takaice a cikin rahoton ta bayyana yadda wasu 'yan asalin kasar Baman mazauna Washington suka gudanar da zanga-zangar rashin amincewa da Allah wadai da kisan gilla da ake yiwa Musulamai 'yan kabilar Rohingya wanda 'yan addinin Budha tare da hadin guiwar Sojoji da hukumomin kasar ke aikatawa. A inda abu ne mawuyaci ka bayyana hakikanin abin da yake faruwa a Kasar.
Musulmi kasar Bama da kyar suke samun cokali hudu na abinci a duk kwanan duniya. Ba su da hanyar samun ruwa mai kyau balle hanyar ganin Likita. Kisan gilla, Fyade, kona mutane yana daga cikin abubuwan da suke faruwa ga Musulman kasar musamman a kauyuka.
Dabi'ar Sojojin kasar da 'Yan Sanda ba shi da bambanci da na 'yan ta'addan ISIS da Nusra. Duk wannan na faruwa ne sakamakon goyon bayan da gwamnatin kasar take baiwa 'yan addinin Budha, Sojoji da 'yan Sandar kasarta wajen murkushe Musulmai.
A cikin rahoton ta bayyana cewa; al'amarin ya canza salo daga muni zuwa matsananci muni (abin ya munana). Kananan Yara Mata masu shekaru 8, 9, zuwa 10 ba su tsira daga fyade ba. Wasu daga cikinsu bayan an musu fyade a kashe su, wasu kuma a maishe su bayin da ake biyan bukata da su.
Rusa Masallatai da wulakanta Alkur'ani mai girma duk yana daga cikin ayyukan wadannan 'yan ta'addan. A satin da ya gabata, an rusa kauyuka, an maishe su filaye, an bugi matayensu, an yiwa wasu fyade.
Duk da halin musgunawa da ake yiwa Musulmai a kasar, amma duniya ta yi shiru kamar ba abin da yake faruwa.
-Ammar Muhammad Rajab
5 Ga Watan Nuwamba, 2016.

Comments
Post a Comment