KOTU TA BA DA BELIN ‘YAN UWA 15 A JOS
Daga Saifullahi M. Kabir
Wata Kotun Majistare a garin Jos a karkashin mai shari’a H.T Esg (SDJ) ta bayar da umurnin sakin kananan yara guda 13 da kuma masu rauni (manya) guda biyu daga cikin ‘yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Zakzaky guda 47 da gwamnatin jihar Filato ke tsare da su tun bayan harin da jami’an tsaron Soji da ‘yan Sanda suka kai akan Muzaharar Ashura a ranar Laraba 12/10/2016.An ba da belin yaran ne bayan da suka kwashe sama da kwanaki 23 suna tsare a hannun ‘yan Sanda a ‘A Division’ da ke garin Jos, a yayin da masu raunin kuma suke tsare tsawon wannan kwanakin a ‘State CID’ duk a garin na Jos.

Tuni dai yaran wadanda 9 daga cikinsu ‘yan garin Saminaka ne, 4 kuma
Jos, da kuma masu raunin suka isa gidajensu a daren yau Juma’a
11/4/2016, bayan da aka shirya musu kwarya-kwaryar walima a gidan Shaikh
Adamu Tsoho a yammacin nan. Sai dai abin takaici, da yawa daga
iyayen yaran mata suna kulle a gidan yarin garin na Jos. Hafiza Basiru,
14 ta dawo gida a yayin da Mahaifiyarta Malama Khadija ke tsare, duk da
karamin ciki da take dauke da shi. Haka ma Khalisa M. Kabir da Fatima M.
Kabir duk sun fito ne alhali Mahaifiyarsu Malama Karima na tsare.
Kotun bata ba da belin ragowar ‘yan uwa 32 da ke tsare a Kurkuku ba, cikinsu kuwa har da mace mai ciki wata 8 da mai wata 2 da kuma mai shayar da jariri dan kasa da watanni uku

Comments
Post a Comment