KWAMITIN SADARWA 'MEDIA' NA MATASA YA GUDANAR DA TARO A ZARIYA
Daga Ammar Muhammad Rajab
Da yammacin yau Juma'a, kwamitin Media na Harkar Musulunci a Nijeriya a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky na yankin Halkar Haidar suka gudanar da taro na musamman dangane da abin ya shafi kafafen sadarwa.

Taron ya gudana ne a
sabuwar Fudiyyah dake karamar hukumar Sabon Garin Zariya. Bayan bude
taro da addu'a, karatun Alkur'ani Mai Girma. Ammar Muhammad Rajab
shi ne mai jawabi na farko a wurin taron, inda ya gabatar da jawabi
akan 'Ci Gaban Da Aka Samu Daga Sa'kar Sama (Internet)'. A cikin
bayaninsa ya kawo tarihin samuwar 'internet' da kuma yadda aka fadada
shi har farar hula ya fara amfana da shi. Har wala yau a lokacin da yake
bayani dangane da ci gaban da aka samu, ya nusasshe da mahalarta taron
yadda aka samu ci gaba ta fuskancin ilimi, yin karatu, kasuwanci,
labarai cikin sauki, wallafa bayanai daban-daban da ya shafi al'umma da
sauran su.
Sannan ya kawo yadda samuwar sakar sama (internet) har ya kawo ci gaban da aka samu na samuwar shafukan sada zumunta da yanzu ake amfani da su wajen bayyana ra'ayoyi, ilmummuka, tunatarwa, labarai da rahotanni. Ya ce; a yanzu zamani ya canza har an zo wani lokaci da yanzu abu na faruwa kana iya ganin rubutaccen bayanan, hotuna da kuma bidiyo. Sannan ya lurantar da mahalarta taron yadda samuwar sakar sama ya kawo sauki a rayuwar Bil'adama ta fuskancin aika sako da karbar sako.
Har wala yau a wani bangare na jawabinsa, ya jaddada cewa; yanzu mafi yawan gidajen jaridu, Talabijin da Rediyo zaka same su suna shafukan sakar sama, ko kuma na sada zumunta wanda samuwar sakar saman ne ya samar da shafukan sada zumuntan. A wani jawabin nasa, ya yi musu bayani dangane da GPS da asalin kirkirarsa da dalilin kirkira. Sai ya lurantar da su a kai.
Mai Jawabi na biyu, Malam Abdulhamid Musa Rayyan ya gabatar da jawabinsa ne akan muhimmancin rubutu da ka'idojinsa. Cikin jawabinsa ya nuna rubutu a matsayin wata hanya ce da ake amfani da haruffa wajen isar da wani sako da ya shafi mu'amala, zamantakewa, addini, siyasa, da sauran su. Sannan ya bayyana cewa; a lokacin rubutun ana amfani da alamomi wanda kowanne alama na isar da wani sakon ne. Misali; alamar hutawa, alamar tsayawa, alamar maganar wani da sauran su.
Har wala yau a wani bangare na jawabin ya jadadda muhimmancin rubutu. Sannan ya tabbatar da cewa; duk abin da ka rubuta ko da da wasa ne, za a rika tuna ka da wannan rubutun. Ya ce; kuma wasu rubutun zai yi musu tasiri, wasu kuma zai canza su, duk sakamakon abin da ka rubuta.
Dan uwa Mustapha M. Sani shi ne ya rufe taron da addu'a bayan an kammala jawabai. Sista Zakiyyah Musa, Na'imah Yunusa sune suka gabatar da masu jawabi a wurin. A inda tun farkon taron Dan uwa Bashir Musa ya gabatar da jawabin maraba.
-Ammar Muhammad Rajab ya hada mana rahoton.
4 Nuwamba, 2016.

Comments
Post a Comment