Mun fara tattaunawa da Gwamnatin Tarayya kan sakin El-Zakzaky - NHRC

Mun fara tattaunawa da Gwamnatin Tarayya kan sakin El-Zakzaky - NHRC



Babban Sakataren Hukumar kare hakkin bil' adama ta Najeriya (NHRC), Prof. Bem Agwe ya yi karin haske dangane da matakan da Hukumar ke dauka don ganin an saki Shaikh Ibraheem Zakzaky, Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya.

Agwe dai ya ce babban aikin Hukumar shi ne tabbatar da cewa an sasanta duk wani cin zarafin dan Adam da abin da ya dangance shi wanda kuma batun El Zakzaky shigen irin wannan ne, saboda haka ne kuma suka samar da wani kwamiti da zai yi binciken batutuwan da ke tattare da  tsare da Jagoran yan Shi'ar.

Yayin da yake yi wa mabiyan El Zakzaky bayani, lokacin da suka yi gangamin lumana a gaban hedikwatar Hukumar da ke Abuja ranar Alhamis, Daraktan ba da kariya da bincike na Hukumar, Mr. Abdulrahman Yakubu, wanda ya yi magana a madadin Mr. Agwe; ya yi musu alkawarin sakin Jagoransu.

El Zakzaky dai na tsare ne tun bayan wani harin da sojojin Najeriya suka aikata a kan Mabiyan Harkar ta Musulunci a garin Zaria, Jihar Kaduna.

Tsare shi din da aka yi ya janyo muzaharori daga mabiyan sa, da kuma Allah wadai daga mafi yawan kasashen 'yan Shi'a na duniya.

Comments