RIYA HARAMTA HARKAR MUSULUNCI A JIHAR KADUNA: Babban Lauyan Nijeriya Femi Falana Ya Yi Bayani Bisa Dokokin Kasa.
Haramta Harkar Musulunci da ake riyawa, ya saba wa doka da tsarin mulki
Cewar babban Lauya Femi Falana (SAN)
Mai karatu ga fassarar daidai inda Lauya Falana ya yi wannan maganar sa'lin da yake jawabi a wani taron kare hakkin 'yan jarida a Ikko a makon nan.
Lokacin da sojoji suka kashe 'ya'yan Shaikh Ibraheem Zakzaky, Shugaban 'yan Shi'a, guda uku a shekarar 2014, El Rufa'i ya kai masa ziyara a gidansa da ke Zaria. Har wala yau, ya je gidan domin neman goyon bayan 'yan Shi'ar su zabe shi a takarar Gwamna da ya fito a shekarar 2015. Sannan lokacin da ya ci zaben ma sai da ya tura 'yar uwarsa ta yi wa Shaikh din godiya.
Amma bayan harin ta'addanci da sojoji suka aikata a kan 'yan Shi'ar a watan Disambar 2015, gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da dama aka binne 'yan kasa 348 wadanda Sojojin rike da muggan makamai suka kashe. Har wala yau, gwamnatin ta Kaduna ta rusa gidan Shaikh Zakzaky da sauran muhallan 'yan Shi'a.
Duk da cewa har yanzu gwamnatin ba ta fitar da farar takarda kan rahoton kwamitin binciken kidan da sojojin suka yi wanda mai shari'a Garba ya jagoranta ba; amma Gwamna El Rufa'i ya bayyana haramta Harkar Musulunci a Najeriya.
Sojoji da yan sanda sun kashe mutane da dan dama a wancan satin da sunan kiyaye sabuwar dokar. Da taimakon jami'an tsaron, matasa 'yan banga suka kona muhallan 'yan Harkar da dama. Gwamnatin ta Kaduna ta ce ta dogara da sashi na 45 ne na tsarin kundin mulki wajen haramtawar.
Tare da girmamawa, gwamnatin jiha ba ta da ikon haramta kowace irin al'umma a Najeriya. A shari'ar Dakarun Zaman lafiya da Sufeto Janar na 'yan sanda (2012), babbar kotun kasa ta tabbatar da cewa haramt masu karar ba tare da odar kotu ba, lallai babu shi a doka. Saboda haka, wannan haramcin wai da aka ce an yi wa Harkar Musulunci ba daidai ba ne sam kuma ya saba wa kundin tsarin mulki.
Da fatan gwamnatin tarayya za ta takawa gwamnatin Jihar Kaduna birki daga neman jefa kasa da take yi cikin wani rikicin addini.

Comments
Post a Comment