Siyasar Amurka: TSAKANIN HILARY DA DONALD TRUMP

TSAKANIN HILARY DA DONALD TRUMP


Daga Ammar Muhammad Rajab


A yau Talata ake gudanar da babban zaben takarar shugabancin kasar Amurka wanda a halin yanzu rahotanni sun nuna cewa; ana ci gaba da kada kuri'a. Kuma da alama 'yar takarar shugabancin kasar a jam'iyya mai ci wato Democrat tana gaba a halin yanzu da kashi kusan 5 tsakaninta da dan takarar jam'iyyar Republican Donald Trump.


Sai dai a ya yin da ake gudanar da wannan zaben, na lura da yawan 'yan Nijeriya musamman a kafafen sada zumunta da a kasar Amurka suke, 'yar gidan Clinton (Hilary Clinton) za su zaba, su jefar da Donald Trump. Ra'ayoyinsu a wadannan kafafe ya nuna hakan. Ba don komai ba sai don a tunaninsu Donald Trump ya fito fili ya nuna kiyayyarsa ga al'ummar Musulmi, a ya yin da ita kuma Hilary ta kame bakinta ta yi gum tana fafatutikar neman ganin an zabe ta. Wani bawan Allah dangane da wannan zaben yana ce min; da bakin-kirin gwara baki-baki, ni ko na ce masa; a'a duka dai baki ne za a kira su.

Zabe ne dai tsakanin mummuna da mafi muni. Sai dai mun zura ido mu ga wa zai ci zaben (mu ga sakamakon zaben zuwa gobe). Amma ga dukkan alamu Mrs ce zata ci zaben. Ga al'ummar Musulmi ya kamata su fahimci shuwagabannin kasar Amurka, shedanu ne, kowa ya ci tsakaninsu babu wanda zai saurara Musulunci da al'ummar Musulmai, illa iyaka ma su fadada ta'addancinsu zuwa sauran kasashen Musulmin da ba a ta'addancin, su kuma ci gaba da kirkiro kungiyoyin ta'adda da sunan Musulunci. Haka ya faru, a lokacin mulkin tsohon shugabar kasar Amurka George Bush ya kaddamar da hare-hare wanda ya kai ga kashe Musulmai bila adadin, wanda ya hada da kanana Yara, Mata, tsofaffi tare da rugurguza muhimman muhallan al'ummar Musulmi. Bayan ya sauka, Barack Obama ya hau, Musulmai suna ta murna, Malamai na ta sharhi wai Musulmi ya zama shugaban kasar Amurka. Amma a halin yanzu ayyukan ta'addancin da Obama ya aikata a tsawon mulkinsa ya fi na Bush muni. Ba don komai a illa suna karbar Umurni ne daga wadansu 'yan tsirarun Yahudawa dake juya kasar. Hakazalika duk wanda ya zama shugaban kasa a halin yanzu (Hilary ko Donald Trump) duk kanwar ja ce, za su dora ne daga inda Obama ya tsaya.

-Ammar Muhammad Rajab
8 Ga watan Nuwamban 2016.


Comments