TA’ADDANCIN SOJOJIN NIJERIYA A ZARIYA: Allah Kadai Ya San Adadin Mutanen Da Aka Raunata.



TA’ADDANCIN SOJOJIN NIJERIYA A ZARIYA: Allah Kadai Ya San Adadin Mutanen Da Aka Raunata. 

Daga Ammar Muhammad Rajab

A ranar wata Asabar, 27 ga watan Agustan, 2016, cibiyar dake fafutikar ganin an saki jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky suka gudanar da wani taro domin tantance adadin wadanda aka raunta a lokacin kashe-kashen da Sojoji suka yi a Zariya tare da tallafa musu da kuma wadanda aka kashe musu mazaje, ‘ya’ya da iyalai.
Taron ya gudana ne a muhallin makarantar Fudiyya dake Zariya. Kuma ya samu halartar mabiya harkar daga sassa daban-daban na kasarnan. 

Malam Abdurrahman Yola, shi ne jagoran cibiyar dake fafutikar ganin an saki jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya bayyana makasudin wannan taron, inda ya bayyana cewa; an shirya taron ne domin tantance adadin wadanda aka raunata a lokacin da Sojojin suka aukawa ‘yan uwa almajiran Shaikh Zakzaky a ranekun 12 zuwa 14 ga watan Disamban, 2015. Sannan ya tabbatar da cewa; daga cikin mahalarta taron harda mata da kananan Yara wadanda yake suna daga cikin iyalan mutane dubu da har yanzu ba a gansu ba, wanda ya zama wasu an kashe su, wasu kuma har yanzu ba a san inda suke ba. Sannan ya ce; “wa su ba su ga mazajensu ba, wasu kuma mazajensu an kashe su, wasu kuma suna wadansu muhallai wadanda yake ma bamu san a ina suke ba. A don haka yasa muka taru a wannan muhalli domin mu jajanta musu akan yau kimanin kusan wata tara ke nan aka raba su da mazajensu, ba su san inda suke ba. Wasu da aka raba su da mazajensu, an bizne su ne ba tare da yardar iyalansu ba, wanda har yanzu suna fatan ganin kan cewa an dawo musu da gawarwakin mazajensu, ‘ya’yansu da ‘yan uwansu domin su yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.” Inji shi.

Dangane da yadda suke tallafawa iyalai da matan da wannan abu ya shafa kuwa, ya tabbatar da cewa; tun farkon lokacin da jami’an tsaron Nijeriya suka fara aukawa Harkar Musulunci a Nijeriya a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky aka samar da wata gidauniya ta musamman wacce take kula da wannan fannin, ya ce’ “kuma daidai gwargwado tana bakin kokarinta wajen ganin ta inganta bangaren dukkan rayuwarsu da ya shafi karatunsu da na ‘ya’yansu.” Sannan ya  tabbatar da cewa; wannan gidauniya an kafa ta ne sama da shekara goma sha. Sannan ya nusasshe da hanyar da suke bi wajen tallafawa wadanda abin ya sha, ya ce; hanyar da suke bi wajen tallafawa iyalan wadanda aka rasa akan wannan hanyar shi ne; tallafin da ake samu daga bangaren su ’yan uwa almajiran Shaikh Zakzaky. Ya ce; “wannan kula kuma ya hada; ‘ya’ya, Iyalai, Mata da Iyayen wanda duk wanda aka kashe ya bari.” 

Dangane da wadanda suka ji raunuka kuwa, ya tabbatar da cewa; “muna da daruruwa ne, wadanda suka kwanta a asibiti, aka yi musu jinya akalla sun kusan dari, akwai wadanda ya zama an sallame su, wannna ma yasa ya zamo muka kira wannan taron da sunan taron tantance wadanda aka raunata, sanin adadin wadanda suka samu raunuka da kuma tsananin raunin na su, don sanin wadanda suke bukatar kulawa na musamman domin kaisu inda ya kamata su samu lafiya. Wannan na daga cikin dalilan wanann taron.” Har wala yau ya kara da cewa; sanin raunukan kowanne ne zai sa su san agaji da tallafin da ya kamata su bashi. Ya ce; a taron akwai Likitoci da za su duba marasa lafiyar da nazartar raunukansu domin su sa su shawarwari. Dangane da lafiyar Malam Zakzaky kuwa, ya tabbatar da cewa; a halin yanzu Malam Zakzaky na bukatar ganin likitansa, saboda yadda ya rasa idonsa daya kuma dayanma a halin yanzu ya fara rasa shi shima. Ya ce; “tunda har likitocin da jami’an leken asiri na farin kaya na DSS suka kawo domin duba lafiyar Malam sun tabbatar da cewa; sun yi iya na su ba za su iya ba, ya kamata a basu Malam Zakzaky domin su kaishi inda za a duba lafiyarsa.” 

Shi ko Dakta Abdulkareem Usamatu, shi ne jagoran likitocin Harkar, wanda yake kula da wadanda aka jikkata shima ya tabbatar da cewa; wadanda suke da su a rubuce akalla suna da sama da mutum tamanin da takwas (88) da suka ji raunuka, ya ce; wadannan adadin har yanzu suna karbar kulawa a asibitoci daban-daban na kasarnan. Sannan ya nusasshe da cewa; wannan adadin banda wadanda suka warke zuwa yanzu. Sai dai ya ce; wasu da yawa sun warke wadanda suka ji raunuka, sai dai mutane 88 din nan ne suka kai ga tantancewa wanda suke asibiti a halin yanzu. Sannan ya yi nuni da cewa; “wasu ma saboda raunukansu baza su iya zuwa taron ba. Sannan wasu ma har ya zuwa yau ba a iya cire harsasan dake jikinsu ba. A halin yanzu wadanda suke kwance mutum 88 ne, wasu an musu aiki, wasu kuma har yanzu ba a kai ga cire musu harsasan jikinsu ba.” Inji Dakta Usamatu.  A karshe ya tabbatar da cewa; wadanda suka nakasa suma ana yi musu tanadi na musamman wajen rage musu radadi. Sannan Iyalai mata da aka kashe musu mazaje, cibiyar dake kula da wannan bangare na Harkar Musulunci, duka tana kula da iliminsu, kula da su, da abin da ya shafi haihuwa da dukkan al’amuran rayuwarsu daidai gwargwado ana yi musu. Sannan ya nusasshe da cewa; ya zuwa yanzu tun bayan kashe-kashen da aka yi, wadanda aka kashewa mazaje, sun haifi akalla jarirai sama da 100. Kuma wannan gidauniya ita take daukar dawainiyyarsu, a gefe guda kuma ‘yan uwa ke daukar dawainiyyar wannan gidauniya.

A lokacin taron, Shaikh Abdulhamid Bello ne ya gabatar da jawabin rufewa, a inda ya karfafa Shahidai masu rai, da Iyalan Shahidai akan su tsaya kyam akan tafarkin Allah. Ya jajantawa Iyalan cikin kuka na rashin cancantarsa ya tsaya a gabansu yana musu bayani. Inda ya bayyana cewa; sun samu wata babban daraja ta musamman. Sannan ya bayyana Shahidai a matsayin wadanda suka tsaya kyam har suka cimma nasara. Har wala yau Shehin Malamin ya ce; duk wanda Allah ya yi masa ni'imar shiriya, ya godewa Allah. Saboda ni'imar shiriya Allah ta'ala ke bayarwa ga wanda ya so. Sannan idan Allah ya baka wannan ni'ima, to akwai gwaji daga Allah, wannan gwajin ne zai sa ka san cewa; kana kan hanyarnan ta shiriya. Ya ba da misali da Annabawa da sauran bayin Allah na yadda Allah ta’ala ke jarabtarsu. Sannan ya nusasshe da mahalarta taron akan cewa; mu da muka rage, akwai Jan aiki a gabanmu na dakewa da tsayawa kyam akan wannan tafarki. Ya ba da misali da Suratul Hud, Wanda Manzon Allah ya ce; Surar sai da ta saka shi furfura saboda yadda Allah ta'ala ya nusasshe shi akan ya tsaya kyam. 

A wani bangare na jawabinsa, ya nusasshe da cewa; dukkan wata jarabawa matakin cinyeta shi ne hakuri. Ya kawo ayoyin Allah ta'ala domin tabbatar da bayaninsa. Sannan ya ce; dukkan masu hakuri da wannan gwaji din, bushararsu tun daga duniya za su fara ganin sakamako, hakazalika za su ga sakamako mai kyau a lahira. Sannan ya karfafi 'yan uwa akan kyautata tsakaninmu da Allah, dagewa da ibada. Sannan kuma da inganta 'yan uwantaka a tsakanin 'yan uwa da kyautata kowa zato. Ya jaddada cewa; matakin nasara shi ne; soyayyar 'yan uwantaka ta inganta a tsakanin 'yan uwa, kuma saboda Allah. "Mu kaunaci junanmu saboda Allah, sai Allah ya taimakemu, mu kiyaye hakkin 'yan uwantaka tsakaninmu. Mafi karancin soyayya ga 'yan uwa, shi ne; ka sowa dan uwanka abin da kake sowa kanka. Idan ma zaka iya ka so danuwanka fiye da kanka." Inji Malamin. Sannan ya karfafi ‘yan uwa akan muhimmancin kyautata alaka tsakaninsu da sauran al’umma domin guduwa tare a kuma tsira tare. Ya ce; Manzon Allah Rahama ne ga dukkan talikai, mu yiwa al’umma da’awa da kyawawan dabi’u.

Comments