Muna tir da take-taken gwamnatin Tarayyar na kin bin umurnin kotu kan sakin Shaikh Zakzaky- Mabiya IMN

TAKARDAR MANEMA LABARAI 

Muna tir da take-taken gwamnatin Tarayyar na kin bin umurnin kotu kan sakin Shaikh Zakzaky. 

Yayin da yake mai da martani ga hirar Shugaban Dandalin yada labaranmu da sashen Hausa na BBC, Kakakin fadar Shugaban kasa a kan harkar yada labarai, Garba Shehu a ran Litinin 02/01/17 ya yi wasu kalamai masu nuna take-taken Gwamnatin Tarayya na kin bin umurnin hukuncin da babbar kotun Abuja ta 6 ta yanke na a saki Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky a cikin kwanaki Arbain da biyar daga ranar da aka yanke hukuncin. 


Ya bayyana cewa wadansu mutane sun daukaka kara a kan hukuncin da babbar Kotun Abujar ta yanke ba tare kuma da ya ambata ko su wane ne su ba. Ya kuma ambata cewa wasu dalilai na tsaron kasa da bai bayyana takamaimai ko wadanne nen ba su ke sa ake ci gaba da tsare Shehin Malamin ba bisa kaida ba. Haka nan kuma ya nisanta Shugaban kasa a kan hannun da yake da shi cikin lamarin, a inda ya bayyana cewa lamari ne wanda ya shafi gwamnatin Jihar Kaduna.

Wannan ba shi ne karon farko ba wanda mai taimaka wa Shugaban kasa a kan harkar yada labarai ya yi kokarin nisanta hannun Shugaban kasa a kan lamarin Kisan Kiyashin da aka kaddamar a garin Zariya. Amma alal hakika babu wata hujja da za ta iya wanke Shugaban daga hannun da yake da shi a kan tsararrun hare-hare na taaddanci da ake kai wa yan uwa Musulmi na Harkar Musulunci a Najeriya a cikin daukacin kasar ta tarayyar Najeriya. Tsakanin rundunar Sojojin Nijeriya da suka fara kaddamar da kisan kiyashi a garin Zariya da kuma Hukumar Jamian tsaro na farin kaya (DSS) wadda ke tsare da Shaikh Zakzaky ba bisa kaida ba, ba wacce take Hukumar gwamnatin Jihar Kaduna. 

Shugaban Kasa dai shi ne babban Kwamandan askarawan Sojojin Najeriya kuma babban Jamiin tsaro na kasa baki daya. Sai ga shi ya kasa daukar mataki a kan wadanda suka yi fatali da dokokin kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya gabansu gadi, ta hanyar kashe yan kasa fararen hula wadanda ba su dauke da makami tare kuma da yi wa gawawwakinsu kabari na bai daya, kamar yadda rahoton hukumar binciken kisan kiyashin Zariya (JCI) ya tabbatar.

Kasantuwar Shugaban Kasa ya kasa ko da yi wa dangin wadanda aka kashe taaziyyar jajen rashin yan uwansu da suka yi, ko kuma nuna tausaya wa ga wadanda aka jikkata a yayin harin, ko da kuwa a bayan da hukumar bincike ta (JCI) ta fitar da rahoton da ya tabbatar da kisan daruruwan yan kasa fararen hula da jamian tsaro Sojoji suka yi, alhali kuma shi ne babban kwamandan askarawa, ba zai iya tsame hannunsa a cikin wannan taannuti ba.

Dadin dadawa kuma, Mai taimaka wa Shugaban kasa sai ya nuna jahilcin cewa Antoni-janar na tarayyar Najeriya, wanda yana cikin wadanda ake kara kan tabbatar da hakkin Shaikh Zakzaky, Ministan Tarayya ne da ke wakiltar Shugaban kasa a cikin wannan kara.

Haka nan kuma, irin girma da fadin hare-haren taaddancin da ake kaddamarwa a kan yan uwa Musulmi na Harkar Musulunci a Najeriya (IMN), ai bai tsaya a iya cikin Jihar Kaduna ba, amma wani tsararren shiri ne da wasu jihohi suke taimakawa a sarari wajen aiwatarwa. Salon harin taaddancin da aka yi amfani da shi a Kano, Jos, Sakkwato, Funtuwa da kuma Kaduna ai ba lamari ba ne wanda ya shafi jihar Kaduna ita kadai ba, kamar yadda Garba Shehu ya yi ikirari. Don haka a sani lallai ba za a yaudare mu da shirun da gwamnatin tarayya ta yi ba a kan wannan lamari na tsawon sama da shekara guda.

Mai taimaka wa Shugaban kasar ya yi kuma kokarin danganta tsare Shaikh Zakzaky da batun da ya shafi wasu zarge-zarge marasa tushe na tsaro. Wanda kuma dama wannan dalilin shi ne wanda mahukunta suke bayyanawa a duk lokacin da ruwa ya karewa dan kada. Ta yaya ne bin umurnin kotu na sakin wanda aka tsare a boye na tsawon sama da shekara guda zai iya zama barazana ga
shaanin tsaro? Mun yi amannar cewa babu wani batu na shaanin barazana ta tsaro da zai sanya a ci gaba da tauye wa Shaikh Zakzaky yancinsa. Hukumomi sun kasa aza wani laifi a kan Shaikh Zakzaky da iyalinsa a tsawon shekara guda da ya yi a tsare.

Da yake bayyana dalilin da ya sanya ba su bi ba, kuma ta yiwu ba za su bi umurnin kotun ba, ya ce wasu mutane sun daukaka kara a kan hukuncin, amma kuma ya kasa bayyana su waye su kuma bisa wane dalili. Abin sani dai a nan shi ne, mujarradin daukaka kara kawai ba zai iya dakatar da zartar da umurnin waccan kotun ba, sai dai kawai idan wata babbar kotu ce ta bayar da umarni a kan haka. Haka nan kuma bai iya bayyana wani umurni da aka fitar ba wanda ya ci karo da wannan hukunci na sakin Shaikh Zakzaky da Kotu ta bayar ba, duk kuwa da cewa waadin sakinsa na kara kusantowa. A sarari yake cewa gwamnatin dai tana so ta yi wasa da hankalin jamaa ne kawai.

Mun yi amannar cewa maimakon hakan, fadar Shugaban Kasa tana bukatar ta bi umurnin kotu na a gaggauta sakin Jagoranmu, Shaikh Ibraheem Zakzaky a matakin farko, maimakon musanta hannun da tabbas tana da shi a cikin lamarin kisan kiyashin da aka kaddamar a garin Zariya, ko fitar da wasu damuwa na ba gaira ba sabat kan shaanin tsaro. A dai yi mu gani, domin kuwa al'umman duniya suna ji kuma suna gani.

SA HANNU:
IBRAHIM MUSA
SHUGABAN DANDALIN YADA LABARAI NA HARKAR MUSULUNCI A NAJERIYA
07/01/2017
Skype: Ibrahim Musa42
Fassara daga Zaharaddeen Sani Malumfashi



Comments