Zababbun zantuka 25 daga jawabin Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky
MENE NE MUSULUNCI? WANE NE MUSULMI?
Zance na daya; “mene ne Musulunci? Kuma wane ne Musulmi? Musulunci shi ne yarda da kuma aikata sakon da Manzo Allah Muhammad (S.A.W.W) ya zo da shi daga wajen Allah. Musulmi shi ne wanda ya yarda yake kuma aikata sakon da Allah (T) ya aiko Manzonsa Muhammad (S.A.W.W) da shi.”
ABUBUWA UKU SUN HAU KANMU
Zance na biyu; “me ya rataya a wuyanmu a matsayinmu na Musulmi? Na farko: ya rataya a wuyanmu mu san addinin nan. Na biyu: ya rataya a wuyanmu mu aikata addinin nan. Na uku: ya rataya a wuyanmu mu kira sauran mutane zuwa ga addinin nan. Mu duba mu gani ya zuwa wane mikidari ne muka rike wannan dawainiyyar?”
CIKIN KASHIN MUTANE UKU A ’YAN WANNE KAKE?
Zance na Uku; “idan kira ya bayyana, ‘ADATAN’ mutane sukan rabu kashi uku ne. Daya kalilan masu kira, kashi daya kalilan da suka ce; lallai da mu za a yi, su sha wahala. Sai kuma ‘Majority’ ‘yan kallo, mu ga wanda ya ci riba (wanda ya yi nasara tare muke da shi). Su suna tare da mai karfi ne. Idan masu kira ga addini suka yi nasara sai su zo su yi basha da baki, su ce; ai daman mun san kuna kan gaskiya ne, ko da kuka gani ba mu zo an yi da mu ba, muna tare da ku a zuciya, gangar jiki ne kawai ba mu kasamce tare da ku ba. In kuma aka murkushe masu addini, sai su ce; to, haba rigima kawai gidi-gidi da kai wai addini, ga irinta nan. Haka jama’a sukan kasu.” A lokacin Fir’auna da Musa, jama’a da yawa sai suka bi Fir’auna kalilan suka bi Musa suka sha wahala, wasu kuma suka ce, In dai Musa ya yi nasara muna tare da shi, in kuma Fir’auna ya yi nasara muna tare da shi. Su suna bin mai karfi ne. To, idan ka zama dan zura ido, kila idan an yi nasara, ka yi sa’a ka zo kai basha da baki ka ce; da kai za a yi. Haka ma lokacin Manzon Allah abin ya faru. Da farko wasu sun tsaya tare da Annabi suka sha wahala, wasu ko aka tursasa musu, wasu kuma ‘yan kallo ne. Amma kuma can karshe da addinin ya yi nasara sai kuma kowane ya zo ya ce; da shi za a yi. To idan ma ya gani ke nan. To idan mutum aka rafke shi ko ya mutu kafin lokacin fa? Tana iya yiwuwa mutum bai ga nasarar ba ya mutu. Ya ce mene ne? Ka ga zai ce wa Allah ne ai na san su ne da gaskiya amma kuma ban taimaka ba sai kuma na yi rashin sa’a na mutu? Wato a takaice dai zabi ya zama na mutum, ko ya yanke shawara ya ce; da shi za a yi, ko ya zura ido, ya rage masa. Amma dai tabbatar addini insha Allahul Azim kamar ya tabbata. Muna rokon Allah (T) ya taimake mu da taimakonsa.”
ME YA HADDASA RABEWAR MUSULMI GIDA BIYU?
Zance na hudu; “da yake muna makon hadin kai ne, sai mu ce; a nan ne aka rabu biyu. Saboda haka muna so mu hada kai, tunda muna so mu hada kai ne, sai mu yi wata magana wadda za ta yi daidai da fahimtar kowa da kowa, sai mu ce; Manzon Allah (saww) shi ne Manzon karshe, babu Annabin da zai zo, amma bayansa sai aka dare aka zama biyu a kan al’amuran wulaya. Wasu suka ce; lallai Manzon nan da zai rasu ya rasu ne ya yi shiru bai ce wa al’umma bayana ga wanda za a bi ba. Saboda haka Ahlus Sunnah suka ce; sai aka hadu aka yi shawara sai aka zabi halifa. Amma idan muka tambaye su muka ce; shi halifan nan Annabi ne ya zabe shi? Me za su ce mana? A’a, Annabi ba ruwanshi da wannan ya tafi abin shi ne, shawara aka yi aka zaba. Shi’a sai suka ce; ba mu da wata matsala dangane da wannan, Annabi ya yi mana bayani ya ce; bayanshi Ali ne za a bi. Yadda Manzon Allah ya tafiyar da addini haka zai tafiyar da shi. Tunda muna makon hadin kai ne, kuma wasu wurare an samu sabani, wannan bangaren, Manzon Allah ya mutu bai ce wa kowa komai ba, wannan bangare bai mutu ba sai da ya tabbatar ya dora (zan bar muku abin da idan kuka rike ba za ku bace ba), ya dora mu ya ce mana ga Shuwagabaninmu nan. Wannan bangaren yana ta fafutikar ya samu Shugaba ko ya bi shi, wannan bangare shi ba ya neman Shugaba don yana da shi, saboda yanzu muna makon hadin kai ne, yanzu za mu hada kai! Da mai Shugaba da mara shugaba! Muna da guda daya su kuma suna da Dubbai, yanzu mu zo mu zauna lafiya, ka bi Shuwagabaninka, na bi Shugabana, amma sunanmu mene ne? Musulmi ‘yan al’ummar Muhammad (s.a.w.w.). Ranar da duk kake so ka bi Shugabana, masha Allah dama can shi ne shugabanka ba ka gane ba ne.”
-Ammar Muhammad Rajab
Daga Shafin Jawaban Shaikh Zakzaky

Comments
Post a Comment