'YAR UWAR SHAIKH ZAKZAKY RAYUWARTA TA SADAUKAR SABODA WANZUWARSA

'YAR UWAR SHAIKH ZAKZAKY RAYUWARTA TA SADAUKAR SABODA WANZUWARSA
'Yar Uwar Shaikh Zakzaky, Gwaggo Fatima ta ba da rayuwarta wajen kare 'dan uwanta, Shaikh Zakzaky a gidansa dake Gyallesu a ranar 12-15/12/2015. An kona ta da ranta a wannan rana. Kafin a kai ga watsa musu fetur a inda suke a kuma kunna musu wuta, ta kalli Sojojin ta bayyana musu cewa; yanzu burin kashe ta suke da shi? Duk da ta manyanta, Dattijuwa ce, amma ba su damu da me ta ce ba, suka kunna mata wuta suka kawo karshen rayuwarta.

Tabbas ta zama ramzi a tsakanin 'yan uwan jini da ma'abota gwagwarmaya na yadda 'yan uwantaka take a Musulunci, wanda ta kaima har ta Sadaukar da rayuwarta kacokaf ga dan uwanta. Ga ma'abota gwagwarmaya kuwa, dakewa da sadaukarwa zai zama a cikin jinin su. Lallai Mazalumiyarta bai zama labari ba a cikin wannan duniya ta Nijeriya.
Lallai na lura da wani abu a duniyan ga, musamman duniyar Nijeriya kullum sharri shi ne labari. Kuma ga al'ummar kasar sun fi karkata ga karya fiye da gaskiya. Misali: 'Dan uwan Zakzaky ya jidadin abin da Sojoji suka yiwa dan uwansa. Sun dauki labarin duuuuuu, domin dakushe tsiron da Allah ya yi da kansa. Ta'ammuli a shafukan sadarwa na zamani yasa na kara fahimtar zancen wani Malaminmu da ya koyar damu darasin 'News Reporting', yake bamu misali da irin labaran da mai karatu ya fi karkata da shi da yadawa a tsakankanin al'umma. Ya bamu misali da cewa; kaine ka zo wucewa sai ka ga kanun labari a Jarida a wurin masu siyar da ita, an rubuta kamar haka: "ZAKI YA CINYE MUTUM', ya ce: wannan labari ne da ba zai siyu a wurin mai karatu ba. Saboda me? Saboda dama hankali ya san cewa; Zaki zai cinye mutum. Ya ce; amma idan ka ga kanun labari an rubuta 'MUTUM YA CINYE ZAKI', ya ce; wannan kanu ne da kowa zai so ya karanta yadda mutum ya cinye Zakin. Kuma mai karatu ya fi bukatarsa. Domin abu ne na al'ajabi da mamaki.
Ina ga wannan yana daya daga cikin dalilan da yasa karya, yarfe, sharri, tuggu da makirci ya yawaita a cikin 'yan Jaridar yau duk don a siya labarin su.
-Ammar Muhammad Rajab
05022017

Comments